5 Satumba 2020 - 11:59
Amurka Zata Rage Tallafin Da Take Bawa Kasar Habasha

Gwamnatin kasar Amurka za ta rage yawan tallafin da take bawa gwamnatin kasar Habasha da dalar Amurka kimani miliyon $100 saboda rashin hada kai da kasashen Sudan da Masar dangane da ginawa da kuma cika madatsar ruwa ta Renainsance.

ABNA24 : Kamfanin dillancin labaran reuters ya nakalto wata majiyar majalisar wakilan kasar Amurla tana fadar haka a ranar Laraba.

Labarin ya kara da cewa ragin ba zai shafi tallafinda Amurka take bayarwa dangane da ‘yan gudun hijira, yaki da cutar HIV/AIDS, ko kuma na annoban dabi’a ba.

Kasar Habasha dai tana cikin rigima mai tsanani da kasashen Masar da Sudan saboda fara cika madatsar ruwa da ta gina kan kogin Nilu da ruwa, ba tare da fahintar juna tsakaninta da kasashen biyu ba.

342/